Header Ads

Sports : Kofin Turai: Sterling ya yi bajinta, Ronaldo ya ji takaici

<

Kofin Turai: Sterling ya yi bajinta, Ronaldo ya ji takaici

A karon farko Raheem Sterling ya ci wa Ingila kwallo uku rigis a wasa daya a karawar neman gurbin gasar cin Kofin Kasashen Turai ta 2020, inda suka casa Jamhuriyar Czech 5-0 a Wembley.


Shi kuwa Cristiano Ronaldo ya ji takaicin yadda kasarsa Portugal wadda ya dawo buga wa wasa ta kasa daga ragar abokiyar karawarta a gasar Ukraine, suka tashi canjaras 0-0.

Rabon da wani dan wasan Ingila ya ci wa kasar kwallo uku a wasa daya a filin Wembley tun a watan Satumba na 2010 lokacin da Jermain Defoe ya yi hakan.


Minti 24 da fara taka leda dan wasan na Manchester City, ya daga ragar bakin, kafin kuma Harry Kane na Tottenham ya kara ta biyu ana dab da tafiya hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo ne a minti na 62 sai Sterling din ya kara ta uku, wadda ita ce ta biyunsa, sannan kuma minti shida tsakani ya cike ta ukun, da ya kafa tarihi da ita.

Bayan wasan ya yi nisa a minti na 84 sai dan wasan Czech, Kalas, ya ci kansu bal ta biyar.

Kociyan Ingila Gareth Southgate a karon farko ya sanya Jadon Sancho na Borussia Dortmund, mai shekara 18, a farkon wasa, kuma matashin ya taka rawar-gani.

Callum Hudson-Odoi wanda ya buga wa Ingila wasansa na farko, ya maye gurbin Sterling.

Kuma tun da farko wani matashin dan wasan na Ingila, Declan Rice, wanda shi ma wasansa na farko kenan a tawagar kasar, ya canji Dele Alli.

Nasarar ta ba wa Ingila damar zama ta daya a teburinsu na rukunin farko (Group A), bayan da Montenegro ta yi kunnen doki 1-1 da Bulgaria, a karawar da suka yi su ma ranar Juma'a.

Rukuni na Biyu (Group B)

Portugal ta tashi ba ci a gidanta da Ukraine, a karawar tasu ta farko ta rukuni na biyu (Group B), wadda Ronaldo ya dawo wa kasar wasa a karon farko, tun bayan fitar da su daga matakin 'yan 16 na gasar Kofin Duniya.

Tun daga wancan lokacin Portugal ta yi wasa sau shida Ronaldon bai buga ba.

Sai dai nasarar da Luxembourg ta yi a kan Lithuania 2-1 a rukunin na biyu, ya sa ta zama ta daya a teburinsu.

A ranar Litinin Portugal za ta karbi bakuncin Serbia a Lisbon a ci gaba da wasannin gasar.

Sakamakon Sauran Wasannin na Juma'a

Zakarun Duniya 'yan Faransa sun fara gasar da sa'a bayan da suka bi Moldova har gida suka lika mata 4-1, a wasansu na rukuni na takwas (Group H).

A sauran wasannin rukunin na takwa, Iceland ta bi Andorra gida ta doke ta 2-0, yayin da Turkiyya ta je gidan Albania ita ma ta ci ta 2-0.

Faransa ta kasance a saman teburin, yayin da Iceland take ta biyu sai Turkiyya ta uku.

Kasashe biyu da suka yi nasarar zama a gaba-gaba a rukunansu, za su samu tikitin zuwa gasar ta Turai ta Euro 2020, amma kuma idan Portugal ta kasa samun damar hakan, duk da haka za ta samu gurbin yin wasan da zai iya ba ta damar samun tikitin, bayan kaiwa wasan kusa da karshe na gasar lig ta kasashen Turai (Nations League).
BBChausa.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.
//]]>