Header Ads

Sports : PSG za ta sayi Toni Kroos na Real Madrid

<

PSG za ta sayi Toni Kroos na Real Madrid

Kungiyar kwallon kafa ta PSG na shirin sanya yuro miliyan 68 don sayen Toni Kroos daga Real Madrid ta Spain cikin wannan kaka don maye gurbin Adrien Rabiot da kwantiraginsa zai kare a watanni biyu masu zuwa da Club din.

Wata jaridar wasanni ta OK Diario ta ruwaito cewa, PSG na shirin daukar matakin sauya tawagar ‘yan wasanta ne bayan shan kaye a hannun Manchester United a wasan karshe na zagayen kungiyoyi 16 karkashin gasar zakarun Turai.

Cikin takaddun bukatar sayen dan wasan da PSG ta mika ga dillalin Toni Kross ta amince ta biya shi yuro miliyan 68 ka na kuma ta biya kashi 50 cikin dari na sauran kwantiraginsa da bai kammala karewa da Real Madrid ba.

Kroos wanda ya na cikin tawagar Real Madrid a ilahirin wasanninta da ya kai ga nasarar dage kofin zakarun Turai har shekaru 3 a jere, ya na daga cikin ‘yan wasan Club din da murabus din Zidane a wancan lokaci ya shafa don kuwa kawo yanzu cikin wannan kaka kwallo daya tal ya iya zurawa cikin wasanni 36 ko da dai ya taimaka an zura kwallaye 5.
RFIhausa.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.
//]]>